Buhari ya bayar da umarnin ne bayan ya samu rahotannin da ke cewa, ana zargin Mohammed Umar mai ritaya da karban cin hanci da rashawa tare da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
A makon jiya ne aka kama Umar bayan jami’an hukumar tsaron farin kaya wato SSS sun kai masa samame a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.
Gabanin kama shi, sai da Darekta Janar na hukumar ta SSS, Lawal Daura ya gana da Buhari, inda ya shaida masa cewa Mr. Umar na amfani da sunan shugaban kasa wato Buhari da wasu manyan jami’an gwamnati wajen karban kudade daga hannun mutane da suka hada da ‘yan kasuwa bayan ya razana su.
Wannan lamarin dai ya tayar da hankalin shugaba Buhari, ganin cewa mutumin da ya amincewa ne ke aikata wannan kazamin aikin kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar.
Wata majiyar tsaro ta ce, Umar na daga cikin attajiran da ke sahun gaba wajen mallakar kadarori a Abuja.288